'Yar Shekaru 76 Ta Shayar Da Danta Mai Shekaru 42 Nono

Linda Berrety

Linda Berrety, tsohuwa yar shekaru saba’in da shida 76, ta kawo rudani a shagon cin abinci na KFC, a jihar Mississippi, tsohuwar dai ta bama danta mai shekaru arba’in da biyu 42, nono a bayyanar jama’a.

Hakan yasa mutane masu cin abinci a shagon zama cikin rashin natsuwa. Ita dai matar da danta duk ma’aikatan gidan abincin ne, wanda kuma aka kore su baki daya. Hakan dai ya jawo surutai da dama, wanda mutane ke magana akan rashin tsari na mata masu shayar da ‘yayan su a cikin jama'a.

A zantawa da akayi da wani da abun ya faru a gaban shi, Mr. Ali Belfouz, “yace bani da matsala da shayar da yara, amma wannan baiyi tsari ba, domin kuwa yaza’ayi ace mace mai wannan shekaru na shayar da kato haka” amma wannan kamar da tabin hankali ciki.

A lokacin da take mai da martani Mrs. Berrety, tace “Hakki ne a matsayina na uwa na shayar da dana, idan mutane basu gamsu da yadda na tarbiyantar da dana ba, to wannan damuwar su ce, ina son dana kwarai, kuma ina jin dadin tarayya da shi. Ina kuma ganin nayi kokari wajen tarbiyantar da dana, don haka bazan dau walakanci da cin zarafi ba daga jama’a, don kawai na shayar da dana da ya girmi wasu uwayen sai zagi.”