Karatun Digirin-Digirgir A Kasashen Waje Na 'Yayan Talakawa Ne!

Abdulsalami Ibrahim matashi mai karatun digirin digirgir.

Shirin Ilimi mabudin rayuwa na DandalinVOA, A yau mun samu zantawa da Abdulsalam Ibrahim. Wanda yake dan shekaru 30 da haihuwa, yanzu haka yana karatun digirin digir-gir a fannin tsarin Manhajar makarantu. A jami’ar Indiana a jihar Pennsylvania, ta nan kasar Amurka. Ya bayyanar muna da babban dalilin da yasa yayi karatu tun daga matakin sakandire har zuwa jami’a, wanda yanzu haka yake karatun karshe a fanin karatun boko, wanda ake cema Likitan Ilimi “Doctor of Education” a turance.

Shi dai mutun ne mai sha’awar aikin malunta, domin kuwa ya fahimci cewar ta aikin koyarwa mutun na iya tai makama al’uma, fiye da yadda mutane kanyi tunani. Sanin kowa ne, cewar malamai sune ginshikin rayuwar al’uma, don haka yaga da akwai bukatar matashi kamar shi ya shiga wannan fanni.

Ya kuma yi kari da cewar, mafi akasarin matasa na ganin cewar sai dan-wane-da-wane kawai ke iya karatu har zuwa irin wannan matakin, ko kuwa mutane da dama naganin cewar, fita zuwa kasar waje karatu sai na ‘yayan masu hali, a nashi fahimtar da sanayya ba haka bane. Dan kowa na iya zuwa kowace kasa a duniya don karatu, don haka akwai bukatar matasa su tashi tsaye wajen neman ilimi, da kuma sama kan su cewar za suyi wannan karatun don taimaka ma kasar su.

Yayi kari dacewar idan mutun yayi kokari tun a makarantar sakandire, zuwa jami’a yasamu sakamako wanda ya kamata, to a zahirin gaskiya zai iya samun gurbin karatu a makarantu har da zasu dauki nauyin karatun shi, a kasashen da suka cigaba, domin kuwa wadannan kasashen suna so su ga mutun nada hazaka, sai su bashi duk goyon baya da yake bukata a karatun shi.