Labarai da ke fitowa, na nuni da cewar shahararren zakaran wasan kwallon rami wadda ake kira “Golf” a turance wato Tiger Woods, za'a yimi shi aiki a gadon bayan shi a karo na biyu. Wannan yasa abokan wasan shi cikin mamaki mai zurfi.
Dan wasan dai ya dau alwashin dawowa a kakar bana, don buga wasa, yace hutun da ya dauka dama domin yaje yawon shakata wane. A tabakin abokan wasan na shi, suna da yakinin cewar, shi zakara ne kuma duk da rashin lafiyar tashi, idan yaso ya buga wasan zakaru na kamfanin motocin BMW, zai iya kuma zai iya yin nasara. Kana abkwai tabbacin zai iya yin nasara a kan duk wani gwarzo cikin su.
Shi dai dan-wasan mai shekaru 39, ya dai buga wasanni goma sha takwas 18, ne tun daga shekarar 2014 zuwa yanzu, bayan wani aiki da akayi mishi a gadon bayan shi, ya dai bayyanar ma magoya bayan shi a shafin shi na yanar gizo cewar, an sake yimi shi aiki don cire wani kololo dake damun wata jijiya a gadon bayan shi. Amma dai yana cigaba da samun sauki.