Wani jirgin kasar Canada, da ya taso daga kasar Tel Aviv, zuwa Toronto ta kasar Canada, ya canza layi zuwa kasar Germany. Abun tambaya a nan shine, mai yasa matukin jirgin ya yanke shawarar yin hakan cikin kurarren lokaci?
Jirgin ya taso daga yankin kasashen Larabawa zuwa kasar Canada, amma ana cikin haka sai matukin jirgin ya fahimci cewar, ingin din dumama dakin jirgin baya aiki, wanda yasa wani kare mai suna "Simba" ya kama rawar sanyi. Shi dai wannan Karen mai shekaru bakwai 7, a cewar matukin jirgin, idan ya cigaba da tafiya kamin su kai masaukin su, yana iya mutuwa sabo da yanayin sanyi, don haka yaga yafi kamata ya juya akalar jirgin, zuwa kasar Germany, domin kuwa yana da yakin cewar idan suka isa can, zasu iya samun wani jirgi da za’a sa Karen da mai Karen.
A sakamakon juyawar jirgin yasa mutane dake cikin jirgin, sun samu tsaiko na kimanin mintoci 75 bisa yadda aka tsaro tafiya. Daga bisani, an yima fasinjoji cikin jirgin bayani, suma sun gamsu da hukuncin matukin jirgin. An dai yabama matukin jirgin da ceto rayuwar Karen, duk dai da cewar fasinjoji sun samu tsaiko.