Tarihi ya mai-mai ta kan shi a wasan "American Ninja Warrior" na kasar Amurka. Wannan wani wasa ne da ke tattare da wasu fadi tashi, hawa da sauka. Issac Caldiero, matashi da ya kafa tarihi, a wasan da ake gudanarwa a kasar Amurka, a kowace shekara.
A tarihin wasan ba’a taba samun mutun daya da ya taba kaiwa zangon karshe ba, wanda ake bada kyautar makudan kudi da suka kai dallar Amurka Milliyan daya $1. Dai dai da Naira milliyan dari biyu da ashirin 220,000,000.
Babban Abun la’akari shine, a tahirin rayuwar Isaac, bai taba samun kudi da suka kai yawan dalla $9,000, kwatan kwacin Naira milliyan daya da dubu dari tara da tamanin 1,980,000. A shekara, amma sai ga shi yau rana tsaka ya zama mai kudin gaske.
Sama da shekaru bakwai 7, da aka fara gudanar da wasan, sai a wannan shekarar a karon farko aka taba samun gwarzo. A lokacin da yake zantawa da manema labarai yace, “Abun da yabani nasara har na kai karon karshe, ba wani abu bane, illa yadda na nace, da kuma irin karfin gwiwa da nake samu, daga abokai na da 'yan kallo.
Domin kuwa, kowace shekara, sai nayi amma ban hakura ba don na fadi, amma yau a karshe nazama mutun na farko da ya zama zakara. Don haka kowa ma na iya yi idan yasa naci a kowane irin abu a rayuwa.”