Tsohon shahararen dan wasan kwallon basketball, Rex Chapman, zai fuskanci hukunci na tsawon kwanaki talatin da biyu 32, a wani laifin sata da yayi a shagon Apple. Shi dai dan wasan ya amsa cewar yayi wannan satar, kuma kotu ta yanke mishi hukunci cewar zaiyi aikin cigaban kasa na tsawon wadanna kwanaki.
Kana kuma zai biya rabin kudin kayan da ya sata, kamin ya fara wannan hukuncin. Wanda kudin kayan suka kai kimanin dallar Amurka, dubu goma sha fiyar, da dari da ashirin da takwas, da sent talatin $15,128.30. Kwatan kwacin naira milliyan uku da dubu dari uku da ashirin. 3,320,000. Sai kuma ya biya sauran rabin bayan ya kamala hukuncin da aka saka mishi.
Zai kuma shiga aji na tsawon awowi hudu a kwanaki shidda, don a koyar da shi da’a da halin diyauci, a tsawon wasu kwanaki, wanda hallayan da ya nuna a lokacin wannan darasin, shi zai nuna ko kwanaki nawa zai je wannan makarantar don daukan darasi, a cewar kotun.
A shakear da ta gabata ne aka gano cewar wannan dan wasan, ya saci abubuwa har sau bakwai 7 a wannan shagon na Apple, wanda daga bisani yake sayar da kayan ga wani mutun.
Chapman din mai shekaru 47, yace bai iya tuna wadannan satar da akace yayi, sana diyyar wasu magunguna da ya dade yana sha.