Pasto Ya Kashe Kanshi, Da Kunyar Duniya Gara Ta Lahira

Pasto John Gobson

Wani Pasto ya kashe kan shi, da dama zasu yi mamaki, ko suce wai mai zai sa mutun kamar Farfesa John Gibson, zai kashe kan shi, kasan cewar Allah ya bashi komai a rayuwa. Shi dai wannan Pasto din, yana da matarshi da ‘yayan shi biyu, mace da na miji. Ya kasan ce yana koyarwa a wata jami’ar koyar da addinin kiristanci a jihar New Orleans, ta Amurka.

Babban dalilin da yasa wannan Paston, ya kashe kan shi shine, don an samu gano cewar yana da akaunt a shafin da yayi kaurin suna wajen harkar neman mata da mazan banza, da harkar luwadi da madigo da ake kira "Ashley Madison". Kwanaki shida 6 bayana an bankado sunayen milliyoyin mutane, wadanda suke da wadannan akaunt din, a cikin jerin sunayen har da na shi.

Bayan an gano cewar yana da wannan akaunt din, yayi bayani dangane da halin damuwa da ya shiga, kana da dalilin da yasa ya bude wannan akaunt din. Ya dai bayyanar da wannan kuskuren na shi a matsayin abun Allah tur, kuma yace iyalan shi su gafarce shi.

A tabakin matar shi, tace, kawai ta shiga dakin shi sai ta tarar da ya kashe kanshi. Kuma suna da masaniyar halin damuwa da yake ciki, mijin ta ya shiga wani halin ha’ula’I, kuma sun san dalilin dayasa yayi tunanin ya kashe kan shi, shine don yana tunanin zai rasa aikin shi, kuma wannan abun kunya ne babba, domin kuwa ya sadaukar da rayuwar shi, wajen taimaka ma al’uma amma sai gashi bai taimaka ma kanshi ba.