Hukumar leken asiri ta Amurka wato FBI ta shiga wani sabon babi na neman wani farfesa dan kasar China, da ke koyarwa a jami’ar jihar Ohio, ta nan kasar Amurka.
Rahotanni na nuni da cewar, wannan malamin na daya daga cikin wadanda ake ji dasu a duniya kimiyya da fasaha, don haka yasa mu damar shiga cikin masu bincike na kasar Amurka, a duniyar sararin samaniya da ake kira "NASA". A na dai tuhumar shi, don gano wace irin danganta ke tsakanin shi da masu binciken kimiyya da fasaha na kasar China.
Shi dai wannan farfesan dan shekaru hamsin da shida 56 da haihuwa, mai suna Rongxing Li, yabar aikin shi a matsayin malami a wannan jami’ar ta jihar Ohio, ba tare da wasu dalilai ba, a watan Fabrairu na shekarar 2014.
Malamin Li, dai ya sanar da hukumar makarantar cewar, zai bar aikin ya koma kasar shi ta China, don jinyar mahaifiyar shi mai yawan shekaru, tun daga nan babu wanda yasake ji daga gare shi. Wata daya kamin ya bar aikin na shi, ya rubuta ma, hukumar bincike ta sararin samaniya cewar yana so yayi aiki da su a wani bincike da suke yi na duniyar 2020. Wannan shi ne yabama Mr. Li, damar sanin wasu bayanai daga ma’aikatar tsaro wanda suke haramun ga kowa ya bayyanar da su ga gwamnatin China, koma wata kasa a duniya.
Kana kuma, wata daya bayan ya bar aiki, jami’in hukumar binciken cikin gida wato “Homeland Security” ta Amurka, ya binciki matar Mr. Li, mai suna Jue Tian, a lokacin da take kokarin shiga jirgi don barin kasar. Yasamu wani abun ajiye bayanan sirri dauke da wasu bayanan tsaro masu matukar mahimanci, tsakanin ita da mijin ta babu wanda aka gurfanar.