Abubuwan Da Jin-Dadi Da Annashuwa Kan Haifar

Jin dadi

Labarin zuciya a tambayi fuska. Duk yadda muka kokarta wajen ganin munyi dai-dai, kura-kurai wasu abubuwa ne da babu yadda zamuyi mu guje musu a rayuwa. A wasu lokutta mukan samu kan mu cikin wani hali musamman ma idan aka ce mutun yasamu sabon aiki, amma abubuwa ba su tafiyanmasa yadda yake so, ko ace mutane na fuskantar wasu matsaloli da suka shafi soyayyar masoya.

A duk lokacin da abubuwa suka tsaya ma mutun a rayuwa, mafi a’ala shine su dauki wannan a matsayin jarabawa wanda yakamata ya basu karfin gwiwar tun karar koma me nene a gaba, da kuma tunanin zama wani jarimi ko jarima a rayuwa.

Mai da hankali a shafufukan zumunta na yanar gizo, wani abu ne da kan dan-kwafe zuciya, musamman ma ta matasa. Sau da dama matasa kan ga abun da wasu ke sawa a shafufukan su, da suka shafi rayuwar su, kamar hoton sutura, abinci, mota da dai makamantan hakan, wanda a nan sai kaga hasada, kyashi, da bakin ciki na neman rufe ma matasan ido.

Domin kuwa da dama matasa zasu ga wani aboki ko kawa, sun sa wasu hotuna dangane da rayuwar su, wanda su sauran basu da, sai kaga matasan sun fara sa tunani cewar, ko taya suma sai sun mallaki irin wannan daukakar. Wanda hakan kan haifar da matsaloli a rayuwa. Babbar mafita anan itace matasa su kokarta sa kan su cikin wasu abubuwa da zasu amfanar dasu, da kuma al’umar su baki daya. Kamar karatun littafai, koyon wata sana’a, aiwatar da wasu abubuwa da zasu dauke ma matasan hankali daga wasu tunani marasa ma’ana.

Matasa su dinga duba shafufkan yanar gizon abokai don samun gwarin gwiwa, da neman sanin ya za'ayi su yi koyi da wadanda suke gaban su da wasu abubuwa a rayuwa.