Mutumin nan da yafi kowa rashin tsawo a duniya ya rasu. Chandra Bahadur Dangi, wanda ke da tsawon 21.5 inci, a cewar masu rubutun littafin tarihin duniya wato “Guinness World Records” ya mutu a wani asibiti mai suna Samoa na nan kasar Amurka ranar Talata. Ya mutu yana da shekaru Saba’in da biyar 75.
Shi dai dan kasar Nepal din dai yayi fama da ciwon huhu ne, wanda yayi sanadiyar mutuwan na shi. A cewar wannan gidanuniyar rubutun abubuwan tarihi na duniya, suna masu mika sakon ta’aziyar su ga iyalan wanna mamacin. Sun kara da cewar lallai wannan mutumin, tarihi ba zai taba mantawa da shi ba.
A shekarar 2012 ne aka gano wannan mutumin, kuma aka bashi wannan kambu na mutumin da yafi kowa kankanta a duniya, domin kuwa kankanta shi da tsawon shi yayi dai-dai da ace jariri dan wata shida. Domin kuwa a da wannan mutumin dan kasar Philippenes, shi ne mafi kan-kan ta a duniya, sai kawai a cikin wannan shekarar aka samu wannan mutumin da yafi shi kankan ta.
Jim kadan bayan an bashi wannan kambun na mutun mafi kan-kanta a duniya a shekarar 2012, sai gashi an samu wata mata a kasar Indiya mai suna Jyothi Amge, itama tazama mace mafi kan-kan ta a duniya.