Tafiya mabudin ilimi! Mark da matarshi Camille, sunyi shirin yawon duniya, inda suka fara daga yanki Gabashin Amurka, da zummar zagaye duniya. A cewar su, yawon bude ido shine mafi can-cantar hanya da mutun zai more auren shi. Domin kuwa kowa yasan da cewar “tafiya nau’I ce ta wahala, don haka, duk wanda ya iya magance duk wata matsala a lokacin wahala, to lallai wanna zai iya maganin kowane abu yazo masa a rayuwa.”
Don tabbatar da wanna maganar, sun dau alwashin zagye duniya, cikin kwanaki dari uku da sittin da fiyar 365. Mark dai ya kamala digirin shi ta biyu, ya kuma samu aikin malunta a kasar Philippines, wanda suna tare, amma daga baya kuma yasamu aiki a kasar Saudiya.
Sai yatafi ya barta, na tsawon lokaci, amma sukanyi magana a shafin zumunta na facebook, wanda daga bisani yaga cewar akwai bukatar su dawo su zauna tare. Hakan yasa suka shirya wanna tafiya don ganin duniya da kuma kara fahimtar juna a wanna tsakanin.