Amirul-Hajj Ba Aikin Da Kowa Kan Iya Bane

Hajj

Gwamnan jihar Niger Alhaji Abubakar Sani Bello ya sauke mataimakin sa Mohammed Ketso daga matsayin amirul hajj, a ranar da za a fara jigilar maniyatar aikin hajin.
Wata sanarwan da kakakin gwamnan jihar Dr Ibrahim Doba ya bayar, tace an nada kakakin majilisar dokokin jihar Honarabul Aminu Marafa a matsayin sabon amirul hajji.
Wakilin muryar Amurka Mustafa Nasir Batsari ya nemi Karin bayani game da daukar mataki na sai a ranar da za afara jigilar maniyatan ne aka dauki wannan mataki, ga kuma abinda yake cewa.
‘’Ba shakka ada mataimakin gwamna shine amirul Hajji amma kuma a bisa doka mutane 3 din nan sune dokar kasa ta amince su zama gwamna. To kuma tunda gwamna zaiyi tafiya, shi kuma kakakin dama zai tafi makka shi yasa aka ce shi mataimaki ya tsaya ya rike ragamar mulki shi kuma kakaki ya maye gurbin sa, to kaji abinda ya faru’’
To sai dai da wakilin mutryar Amurka Mustafa Nasir Batsari ya tambayi Mai Magana da yawun Gwamnan cewa ko ina gaskiyar cewa cikin hushi ne gwamnan ya sauke shi daga wannan mukamin sai Dr Doba yace wannan ba gaskiya bane.
Har wayau Mastafan yace wa DR Doba to idan haka ne ai shima kakakin na iya maye gurbin Gwamnan don me ba ace ya tsaya ya maye gurbin Gwamnan ba.
Ananko sai Dr Do ba yace ‘’Ai a bisa tsari muddin Gwamna baya nan mataimakin sa shine zai maye gurbin sa’’
Duk da yake ana cewa akwai kyakkyawar fahita tsakaninGwamnan da mataimakin sa sai dai wannan matakin yasa wasu sun dfara sa shakku cikin wannan lamari.