JAMB Ta Fara Sayar Da Fom Na Jarrabawar UTME Ta 2016

Tambarin JAMB

Hukumar shirya jarrabawar shiga jami’o’i da makarantun gaba da sakandare ta Najeriya, JAMB, ta ce ta kammala shirin sayar da takardun neman daukar jarrabawarta ta 2016. Wannan yana kunshe ne cikin sanarwar da babban jami’in yada labaran hukumar ta JAMB, Dr. Fabian Benjamin, ya bayar a Lagos.

Sanarwar ta ce makasudin sayar da takardun neman daukar jarrabawar tun yanzu shine tabbatar da cewa dalibai sun shirya da wuri domin daukar hadaddiyar jarrabawar shiga makarnatun gaba da sakandare, UTME, ta 2016.

An bukaci duk masu niyyar daukar jarrabawar da su sayi katin biyan kudin jarrabawar a bankunan Zenith ko Skye ko kuma First Bank.

Kudin rajistar dai naira dubu 5 ne, sannan masu niyyar daukar jarrabawar zasu biya naira 500 domin sayen littafi mai suna THE LAST DAYS AT FORCADOS HIGH SCHOOL.

Za a ba dalibai wannan littafin a wurin yin rajistar a bayan sun nuna shaidar biyan kudin.

Za a yi rajistar ne daga ranakun 31 ga watan Agusta har zuwa 15 ga watan Janairu. Za a rufe shafin yin rajistar dake intanet a ranar 19 ga watan Janairu.

Jarrabawar kanta, za a fara ta a ranar 29 ga watan Fabrairu, a gama ranar 14 ga watan Maris.