A cewar Mrs. Tammy, ta dauki wani sabon salo wanda take fita da malamanta cike da mota, suje ziyarar bazata gidajen dalibai, don ganin yadda wadanna daliban ke gudanar da rayuwar su tare da iyayen su. Domin tahaka ne kawai, zasu iya fahimtar wane irin hali yaran ke fukanta daga gidajen su, don wanna zai taimaka musu matuka, don sanin ta yadda zasu bi don su taimaka ma wandana daliban.
Ta kara da cewar, a lokkuta da dama, sukan tattauna da iyayen wadanna yaran, idan sunje gidajen su, kuma mafi akasarin lokaci su kan tatauna abubuwa masu mahinmanci, da iyayen yara musamman ma iyayen da basu cika zuwa makarantar yaran su akai-akai ba.
Wasu kuma daga cikin iyayen a wasu lokkuta, sukan bada nasu dalililan na rashin ziyartar makarantar ‘yayan nasu. Wanda za aga cewar wasu suna da dalilai masu kwari, wasu kuwa kawai halin rashin kulawa ne kawai, da rashin damuwa da halin da ‘yayan su suke ciki.
Wanda duk wadanna sukan iya haifar da matsaloli, ga rayuwar yaran idan sun girma, domin basu ga iyayen nasu sun nuna musu damuwa yadda yakamata ba, bayan suna ganin wasu iyayen, suna nuna damuwa ga ‘yayan su. Don haka akwai bukatar duk bangaren, da na iyaye da na malamai su maida hankali, wajen ganin dalibai sun samu kulawa da suka dace da ita, wanda hakan zai sa suma su fahimci rayuwa tun suna ‘yan kananan su.