Rashin Saurayi Ko Budurwa Itace Hanyar Zama Lafiya

Yan mata

An gudanar da wani bincike a tsangayar bincike ta mu’amalar halayyar dan’adam a jam’ar Auchland ta kasar New Zealand. Wanda ya bayyanar da cewar, yana iya kasancewar mutun ya zama mai jin dadi da walwala a lokacin da yake shi kadai batare da budurwa ba, kamar yadda masu 'yan mata suke ji.

A lokacin gudanar da wannan binciken, a karon farko an gwada matasa dubu hudu 4,000 a kasar, wanda kashi daya cikin biyar na wannan, basu da ‘yan mata, sauran kuma kodai masu mata ko masu ‘yan mata. Duk dai a karshen wanna binciken an tambayi irin halin da suka sami kan su, a tsawon wanna shekarar. Rahoto ya nuna cewar babu wani ban-bancin halin rayuwa a tsakanin su, duk da cewar wasu daga cikin su na da abokan hulda.

Kuma wannan binciken ya bayyanar da cewar matasa wadannada basu da ko da saurayi ko budurwa, sunyi hakan ne domin guje ma rashin kwanciyar hankali a tsakanin su da masoya.

Duk wanda yayi kokarin guje ma hatsaniya a tsakanin shi da jama’a, to babu makawa zai kasance cikin kwanciyar hankali, da wadatacciyar lafiya fiye da wanda ke fitina kowane lokaci.

Wannan binciken ya bayyanar da wasu hanyoyi da matasa zasu bi, wajen zaben abokan rayuwa. Abu na farko da yakamata matasa su yi shine, su duba suga wanene wanda bai da son hatsaniya ko yawan magana, kuma da son musu? Duk wanda ya samu kanshi cikin irin wannan tsarin to yana iya zama abokin hulda da kowa.

Idan kuwa mutun yaga budurwa ko saurayi na neman su dinga jayyaya da juna, to kada su kuskura su nemi wannan domin kuwa a karshe suna iya samun rashin fahimta.