Arziki Abun-Ado Talauci Kuwa Sai Gudu

Kiba da Atisaye

Sau da dama idan aka ce “Kiba” sai mutane suyi tunanin jin dadi, ko cin wasu kalan abinci. A wasu lokkuta mutane kanyi tunanin cewar yin kiba shine alamun hutu da jin dadi. Sau da yawa idan akaga mutun yana kiba a kasashen Afrika sai ace yana jin dadi.

A wani bincike da aka gudanar a nan kasar Amurka, wanda ya jagoranci wanna bincike Dr. David Samadi, yace sau da dama mutane kanyi atisaye, don neman rage giba, tunda idan mutane sukayi atisaye sai kitsen dake jikin su da bashi da amfani sai ya kone. Amma ba nan gizo ke sakaba, domin kuwa mafi akasarin masu wanna abun, sukanyi atisaye amma kuma sukanci abinci mai yawa wanda hakan zai sake haifar da wanna kibar.

Abu mafi zaman lafiya shine, mutun yayi atisaye kuma ya rage cin abinci mai yawa a yini. Kamata yayi mutun dan shekaru Ashirin zuwa sama, yaci abinci da za’a ba yara ‘yan shekaru bakwai zuwa goma. A matsayin abincinshi a lokaci daya. Kuma kada mutun ya rasa karin safe, wanna nada ma’ana matuka, kuma mutun yayi kokari wajen cin abinci ya tauna abinci sosai kamin ya hadiye.