More Ma Dadin Rayuwa Lahira Kuwa Gamu Nan Zuwa

Waya a kan hanya

Binciken da aka gudanar kan mutanen da ke amfani da wayar salula yayin da suke tattaki akan hanya, ya nuna cewa kashi 77 cikin 100 na Amurkawa sun ce babu laifi idan mutum ya yi haka.

Sannan kashi uku cikin hudu sun ce babu laifin idan mutum ya duba wayarsa a cikin ababan hawa na jama’a ko kuma idan yana jira a zo kansa a shagunan sayar da kayayyaki.

Sai dai a cewar sakamakon binciken wanda cibiyar Rew Research Centre ta gudanar, kashi 88 cikin 100, na Amurkawa, sun ce bai dace mutum ya rinka amfani da wayar ba a lokacin da ake cin abinci a tsakanin iyali.

Haka kuma bincike ya nuna cewa kusan kashi 94, sun amince da cewa bai dace a yi amfani da wayar ba a lokacin taro kamar yadda kashi 95 ya nuna cewa hakan kuma bai dace ba a cikin sinima ko a wuraren ibada.

Sai dai wani abu da bincike har ila yau ya gano shine, wadanda aka yi binciken akansu suna saba abubuwan da suka fada.