Sabuwar Haukar Zamani Gayu Da Kwar-Kwata

Sabuwar Haukar Zamani

Wata sabuwar dabi’a da matasan wanna zamani, suka mai da ta sana’a. An gano cewar, yadda matasa ke cudanya da junan su musamman ma wajen daukan hoto da kan su da waya, wanda yake sa su na hada kan su da na juna. Wanna sabon salon nada wasu matsaloli da yake haifarwa. A cewar wata likita a jihar Wisconsin ta nan kasar Amurka Dr. Sharon Rink. A duk lokacin da matasa suke kokarin daukar kan su hoto, wanda suke hada kan juna a tare, a dai dai wanna lokacin ne kwar-kwata ke yawo daga kan junan su, musamman ma 'yan mata.

Iyaye kanyi mamakin wai ta ya ‘yayan su ke samo kwar-kwata? Ai kuwa wanna ba wani abun mamakin bane, kasancewar mafi akasarin yaran da ke zuwa makarantar sakandire, sun dauki wanna a matsayin wata hanyar burge abokai. Sukan manta da cewar wanna kan haifar da matsaloli da dama a rayuwar su.

Ta kara da cewar a wanna zamanin matasa kan dauki kansu hoto a kowane lokaci, sabanin yadda akeyi, a da wanda ake samun wani ya dauki hoton.

Hasalima, masana binciken halayyan dabi’un dan’adam, sun gano cewar wanna wata cuta ce, mai matukar damuwa ga rayuwar matasa. Musamman idan matasan suka maida wanna dabi’ar tazamar musu jiki, domin kuwa wanna kan iya taba kwa-kwalwar su matasan.

Duk don kara fahimtar illar wanna dabi’ar, jaridar Mirro News ta ruwaito wani labarin, na wani matashi, mai suna Danny Bowman dan shekaru 19, da yakan dauki kanshi hoto kimanin 200 a rana, wanna yasa har ya kai ga yunkurin kashe kan shi, domin kuwa ya samu tabin hankali. Don haka wanna babbar matsala ce da kan iya haifar da abubuwa da dama ga rayuwar matasa. Don haka akwai bukatar matasa su guji wanna dabi’ar, domin kuwa bazata haifar musu da da mai idoba.