Jaridar "The Sun" ta labarta cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester Uniuted ta matsu sosai a kan ta sayi dan wasan FC Barcelona, Neymar, har ma tana tunanin kashe zunzurutun kudi Fam miliyan 240 domin yin hakan.
A kudin Najeriya, wannan yana nufin Naira miliyan dubu 75, har da wasu miliyan 120 a kai.
Wannan kudi na fitar hankali da kungiyar Manchester United ke son kashewa, ya hada da Fam miliyan 130 da FC Barcelona zata nema domin sayar da dan wasan. Idan aka hada da kudaden harajin sayen dan wasan, sai kudin ya tashi zuwa fam miliyan 165. Sai kuma albashin da shi Neymar zai samu cikin shekaru biyar, watau fam miliyan 75, shine zai tashi a kan fam miliyan 240.
Neymar mai shekaru 23 da haihuwa, zai rika samun albashin fam dubu 300 duk sati. Jaridar The Sun ta ce Manchester United ta yi Imani da cewa kwalliya zata biya kudin sabulu idan ta samu hanyoyi masu kyau na tallata shi Neymar da kuma kungiyar.
Haka kuma, jaridar ta The Sun ta ce akwai rahotanni dake fitowa daga Brazil cewa har United ta gabatar da tayi na fitar hankali na fam miliyan 140, abinda ita ma jaridar The Mirror ta ce ta jiyo.
Sai dai kuma akwai ayar tantama a wannan magana. Jaridar The Sun ta ce majiyoyi da dama a kasar Spain inda Neymar ke bugawa yanzu sun ce yana fakewa da sha’awar da United take nunawa kan sayensa ne kawai domin ya samu sabon kwantaraki mai tsoka daga kungiyarsa ta yanzu, FC Barcelona. Watau dai kamar yana kwaikwayon abinda Sergio Ramos yayi ne.
Ita ma dai kungiyar FC Barcelona ba ta dauki rade-radin cewa zai koma Man U da gaske ba. Shugaban kungiyar FCB, Josep Maria Bartomeu ya fadawa gidan rediyon Catalunya cewar wannan jita jita ce kawai da kuma abinda mutane ke ta rubuce rubuce a kai, amma babu wani tushe cikinsa.