Kare Yayi Rana Wajen Ceto Rayuwar Uban Gidan Shi

Karen da ya ceto Uban gidan shi Mr. Patrick Mulligan

Ai kuwa badan Allah yasa kare na yayi tunani ba, to da rayuwata ta salwanta. A cewar Mr. Patrick Mulligan, ina da yara guda biyu Ryan dan shekaru Goma sha biyu da Lucas dan shekaru Tara. Bisa ga al’ada duk lokacin zafi a kowace shekara, mukan tafi yawon kamun kifi a cikin wani rafi dake kusa da mu. Ranar Asabar da ta wuce, muna cikin ruwa dani da ‘yayan nawa biyu da Kare, sai na fahimci cewar jirgin mu yayi nisa cikin ruwa, don haka akwai bukatar na dawo dashi gefen rafin.

Shiga ta cikin ruwar keda wuya, don na dawo da jirgin baki-baki sai kuwa jirgin yayi gaba da ‘yaya na. Ina ganin su suka yi nisa, kuma gashi bana sanye da rigar kariya wadda take taimakawa don kada abu ya nitse cikin ruwa. Yarana suna ta yawo cikin jirgi, kuma basu iya tuka jirgin ba. Na kai kimanin nisan murabba’I 20 zuwa 30 nisa na da baking gaba. Babban abun tashin hankali shine, gashi na gaji kuma bana samun wata nasara wajen iyo da nake yi.

Sukuma yara na babu wani taimako a kan su, sai na fara salati. Ana cikin haka sai daya daga cikin ‘yayan nawa yace ma Karen, jeka ceto Baban mu sai kuwa karen nan yayi ta iyo, koda ya iso wajen Baban nasu sai kuwa ya juya mishi baya domin yasa mu ya cire rigar kariyar jikin Karen, don ya kubutar da rayuwarshi. Ni har na fara tunanin cewar, babu wani taimako da Karen zai iya yimun, amma daga bisani sai naga cewar wanna Karen yana da hankali.

Sai na sa rigar kariyan jikin Karen, kana kuma ya jawoni domin na gaji bana iya komai, kamin kace wani abu sai gashi Karen ya kawoni inda yara na suke a cikin jirgin ruwan. A takai ce dai wanna Karen shine ya kubutar da rayuwata wanda idan badan wanna Karen ba, tabbas daga ni har yara na da rayuwar mu ta salwanta. Domin kuwa ni zan mutu cikin ruwa, su kuma babu wanda zai kaimu su agaji. Ai kuwa daga yau bazan sake shiga cikin jirgi ba, batare da rigar kariya ba.