Wane Masu Gida, In Ji 'Yan Wasan Nassarawa United

A karon farko cikin shekaru 11 har da watanni, wata kungiyar kwallon kafa ta doke kungiyar Kano Pillars, wadda aka fi yi ma kirari da sunan "Masu Gida" ake kuma ce "Sai Masu Gida", a cikin gidanta, watau filin wasa na Sani Abacha dake Kano.

Kungiyar Nassarawa United, ita ce ta yi wannan abinda shekara da shekaru babu kungiyar da ta iya yi.

Karin abin takaici a wannan kayen farkon, shine tsohon dan wasan ita Kano Piallars, Manir Ubale, wanda a yanzu yake bugawa Nassarawa United, shine ya fara jefa kwallo cikin ragar tsohuwar kulob din tasa, minti 13 da fara wasa, sannan kuma mintoci 3 bayan wannan, ya taimakawa abokion wasansa Bature Yero, ya jefa kwallo na biyu a ragar Pillars.

A cikin minti na 30 da fara wasan ma, Ubale ya yi kusan jefa kwallo na uku, amma aka ce yayi satar fage, ko offside.

Wadannan kwallaye da alamun sun girgiza ‘yan wasan Pillars, amma da aka komo hutun rabin lokaci, Rabiu Ali ya fanso musu kwallo guda. A cikin minti na 67 da fara wasa ma ‘yan wasan na Pillars sun samu kwarin guiwa a bayan da aka shigar da Gambo Mohammed, wanda watanni 5 ba ya iya buga kwallo. Sai dai kuma shigar tasa ba ta tabuka wani abin kirki wajen kara kwallo cikin raga ba.

Wannan kashin farko da aka ba Masu Gida a cikin gidansu, na iya zamowa cikas mafi muni a yunkurin Pillars na sake lashe kambin wasannin Firimiya Lig na Najeriya wanda shekaru ukun da suka shige sun eke lashewa a jere.