Nafi Sha'awar Sana'ar Fina-Finai Da Komai

Tijjani Abdullahi

Tijjani Abdullahi da akafi sani da “Assasing” Wani dan fim din Hausa ne na Kannywood. Mafi akasarin mutane sun fi sanin shi da suna Assassing wato mai kisa. Kafin ya fara sana’ar fim dai, yana yaron mota ne kamin yazo fim indostri. Ya fara sana’ar fim ne a sanadiyar rashi aikin yi, kimanin shekaru ashirin da suka gabata. A da dai, yana ganin ‘yan fim a matsayin wasu bata gari, wadannada basu da aikin yi. Sai daga baya shima yazo ya fara sha’awar shiga cikin fim, a sanadiyar ganin wasu ‘yan wasan suna birgeshi.

Ya kan fito a matsayin mutumin banza a fim, wannan ba shike nuna cewar shi mutumin banza bane a zahiran ce, kawai yakan fito ne a sanadiyar mai bada umurni na sashi a wanna bangare. Su dai babban burin su shine su ilmantar da fadakar da jama’a ta wadanna fina-finan.

Ya kara da cewar, koda an bashi wani fanni da yake mai wahala, yakan kokar ta wajen ganin yayi iya kokarin sa, don ya isar da sakon ga al’uma, batare da yaji wahala ba.

Kuma mutane su sani kowa yake so ya zama mutumin kirki zai iya zama, idan ya so dan haka yana kara kira da matasa, da su kama sana’a kowa ce iri, domin suyi dogaro da kan su a kowane hali suka samu kan su. Wani babban abun sha’awa da wanna sana’ar ta fina-finai shine a na samu alkhairi matuka idan mutun yasa gaskia.