Sabuwar Manhajar Disha Digital Ilimi a Zamanance

Kwamfuta

Ma’aikatar sadarwar kasar Indiya ta kaddamar da wata sabuwar manhajar koyon karatu ga yara ‘yan makarantar firamari da mata, wanda zai tai maka musu wajen kara fahimtar ilimin kwamfuta, yanar gizo, da sauran karatu.

Shi dai wannan manhajar, da ake kiranshi “Disha Digital Litteracy App” a turance, wanna tsarin manhajar, yazo da wasu abubuwa da suka kunshi hotuna don wadanda basu da ilimin kwanfuta, don tahaka zasu samu damar fahimtar me cece kwamfuta kana ta ya zasu yi amfani da wanna na’urar.

Dalilin kirkiro wanna na’urar itace don a tallafawa mata da kananan yara, wadanda basu da ilimin kwamfuta a zamanan ce. Kowa ne mabukaci zai iya amfani da wanna tsarin cikin kudin masu sauki. Kana mutane kan iya zuwa shafin googole domin sabunta wanna manhajar a kowane lokaci.