Majalisar samari ko matasa, tayi kaurin suna da mahadar gulma, kinibibi, gutsuri tsoma, karya, da dai duk abubuwa makamantan hakan. Amma a wasu majalisun kuwa, akan sami matasa da su kanyi firar su ga wasu abubuwan rayuwa don cigaban su da ma ilmantar da juna.
A wanna majalisar da muka ziyarta mai suna “Happy Never End” a turance ma’ana “Jindadi Bai Karewa” inda wadanna matasan su kayi muna bayanin yadda suke gudanar da nasu zaman a majalisa. Su dai su kan zauna a wanna majalisar ne idan sun samu lokaci, kuma su kan tattauna abubuwa da suka shafi rayuwar su da ta abokai, kuma su kan kokarta wajen wayar da kan su da sanar da kai wani abu da wani bai da masaniya akai. A wanna dalilin zaman nasu sun ilmantar da juna matuka domin kuwa, kowa na koyo daga wani bisa ga abun da muka sani.
Amma a wani bangare kuwa su kan yi maganar wasu idan sun zo wucewa, wanda shine mafi akasarin tunanin mutane dangane da majalisa. Musamman ma idan ‘yan mata sukazo suka wuce, suna da bukatar suga macee mai kyau da kuma wadda ta iya wanka da kwalliya. Domin kuwa duk wadda batayi wankan daukan hankali ba, to su babu ruwan su da ita. Babu wanda zai maida hankalin shi ga abunda yake ba abun sha’awa bane ga kowa.
Suna kara kira ga matasa 'yan'uwan su, da suyi kokari suga cewar sunyi amfani da dan kankanin lokacin da suke dashi, a zaman majalisa don karar da juna da wayar da kan juna, ga abubuwan da zasu amfane su baki daya.