Yau 12 ga watan Agusta, rana ce da Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin tunawa da matasa a duk fadin duniya.
Taken wannan shekara shi ne damawa da matasa a fannoni na yau da kullum da suka hada da zamantake da siyasa.
Kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya nuna cewa kowane matashi ya na da ikon samun ilimi mai inganci da samun aikin yi.
“Matsaloli da ake samu na rashin tsaro abubuwa ne da suka shafi rashin ayyukan yi na matasa ko rashin basu kyakyawan tallafi ta fuskar ilimi da damawa da su a siyasance.” In ji Comrade Abdulamjid Babangida Sa’ad, wani matashi mai rajin kare hakkokin matasa.
Sai dai a cewar shugaban Sashen koyar da ilimin kasuwanci a Jami’ar Bayero ta Kano, Farfesa Murtala Sabo Sagagi, , dole sai gwamnati da sauran rukunin masu fada a ji, sun fito da hanyoyi masu dorewa domin samarwa matasa ayyukan yi.
“Dole ya kasance cewa da ‘yan siyasa da malamai da shugabannni na al’uma an duba wai shin menene ma yake janyo wadannan matsaloli na rashin aiki.”
Ya kara da cewa, dole ne sai an yi nazari mai zurfi idan ana so a magance wadannan matsaloli da suka shafi matasa ta hanyar abin da ke da alaka da jiya da yau da kuma gobe.