Tsafta rabin rayuwa, mafi akasarin tsafta anfi alakantata da mata, don haka kuwa duk lokacin da aka ga mace za’a ayi tunanin aga ta kure adaka. Wasu ‘yanmata dake nuni da dalilin da yasa suke yin kwalliya akowane lokaci, ba wani abu bane illa don su gyara kansu ko da sun fita su dinga jawo hankalin samari.
Don sun fahimci cewar samari suna da sha’awar mace tayi kwalliya tayi kyau, sai kaga sunyi sha’awarta. Ai duk maccen da bata kwalliya to ai ba mace bace a tabakin wasu 'yan matan. Domin kuwa a duk lokacin da mace ta fita, zata zama abun kallo ga samari, don haka idan batayi wanna kwalliyar ba, babu yadda za’ayi tayi kasuwa a wajen samari.
A wasu lokkutta kuma sukanyi kwalliyar su ne don su wuce raini a wajen kawayensu, domin kuwa dazarar wata taga cewar kawarta bata gyaran jikinki, to babu yadda za’ayi tayi kawance ma da ita, balle har su jera a kan hanya. Mafi akasarin ‘yan mata kan kashe makudan kudade wajen sayan kayan kwalliya, kana sukanyi amfani da wadanna kayan kwalliya wajen shafe-shafe akalla sau uku ko hudu a rana.