Zaben Shugaban Kungiyar Matasan Najeriya Yabar Baya da Kura

Matasa

A ranar Asabar da ta gabata ne a ka gudanar da zaben shugabanin kungiyar Matasa ta kasa, a babban birnin tarayya Abuja. Bayan kammala wanna zaben ne wasu daga cikin mambobin kungiyar, su kayi korafi da cewarwanna zaben ba a’a gudanar da shi ta yadda ya kamata ba. Don haka akwai bukatar a sake duba wanna sakamakon.

Rahotanni dai na nuni da cewar jami’an tsaro na fararen kaya wato DSS da rundunar ‘Yan sanda ta kasa sukayi awon gaba da wasu daga cikin mambobin kungiyar, a otel din Agura dake tsakiyar birnin Abuja.

A ta bakin tsohon shugaban kungiyar mai barin gado Henry Owabuzo, yace akwai wasu matasa da basu da kishin kungiyar, matasan su ne su kayi kokarin kawo hatsaniya a lokacin da ake gudanar da zaben. Amma a tabakin sakatariyar kungiyar, Halima Tanko Yaro, tayi nuni da cewar wannan zabe da aka gudanar, zabe ne mai inganci domin kuwa jihohi 27 suka samu halartar taron, cikin jihohi 36 da birnin tarayya Abuja. Kuma zababben shugaban Ikenga Ugochinyere, ya samu mafi rinjayen kuri’un da aka kada baki daya.

Sai ta kara da cewar ai sanin kowane cewar, duk lokacin da aka gudanar da zabe za’’a ga cewar, duk wanda bai yi nasara ba, sai ya kalubalanci zaben, don haka wanna bawani sabon abu bane, illa dai kamata yayi matasa suyi kokarin hada kansu a koina suke.