Har Yanzu Ba A Binne Jamilu Abdullahi Ba Amma An Kama 'Yan Civil Defence

Jamilu Abdullahi, dauke da alamun dukar da 'yan Civil Defence suka yi masa a Ofishinsu na Sokoto South

Har yanzu gawar Jamilu Abdullahi tana asibitin koyarwa ta Jami'ar Usman Dan Fodiyo dake Sokoto, watanni fiye da biyu bayan mutuwarsa a sanadin raunukan da ya samu daga mummunar dukar da ake zargin 'yan ofishin Civil Defence a Sokoto ta Kudu sun yi masa.

Sai dai kuma wakilin Ciki da Gaskiya, Murtala Faruk Sanyinna, yace Hukumar Kare Hakkin bil Adama ta Najeriya ta yi ruwa ta yi tsaki cikin al'amarin, abinda ya kai ga kama wasu jami'an hukumar Civil Defence su 4, cikinsu har da D.O. na ofishin Sokoto ta Kudu, wadanda kuma a yanzu haka suke kulle a gidan kurkuku.

Da farko dai su 'yan Civil Defence sun gudanar da abinda suka kira "bincike" inda suka ce marigayin ya buga kansa a jikin garu ko gini ne ya samu raunukan. Amma 'yan sandan da aka sanya su gudanar da bincike, sun musanta wannan ikirarin tare da fadin cewa da ganin marigayin an san lakkada masa duka aka yi.

A bayan da filin Ciki da Gaskiya na VOA ya fara bin sawun wannan kisan gilla, gwamna Aminu Tambuwal na Jihar Sokoto ya bayar da umurnin cewa ofishin mai ba shi shawara kan hakkin bil Adama, ya bi kadin wannan lamarin ya kuma gabatar masa da rahoto a kai.

A kasance da filin Ciki da Gaskiya na wannan makon domin jin karin haske na inda aka kwana, da kuma inda aka dosa game da wannan batu na Jamilu Abdullahi.