Fa'iezza Abdussamad Matashiya Daga Kasar Ghana

Fa'iezza Abdulsamad

DandalinVOA, a yau zai maida hankali ne a kan wasu matasan kasashen Afrika, da su kazo kasar Amrka, don samun horo a fannoni da dama, cikin wani shiri da shugaban kasar Amrka Barak Obama ya kirkiro. Young African Leaders Initiative a turance. Shugaban Amrkan dai ya assasa wanna shirin ne don jaddada demokaradiyya a kasashen Afrika, kana da tsarin shugabanci mai nagarta ga matasan Afrika manyan gobe. Daya daga cikin wadanda suka samu cin gajiyar wanna shirin a shekarar 2015 itace Barista Fa’izza Abdulsamad daga kasar Ghana.

Tafara dacewar an dai haifeta ne a kasar Ghana, wasu daga cikin iyayenta sun fito daga kasar Najeriya wasu kuma Ghana, kana kuma tayi karatun ta na firamari da sakandire a kasar, wanda bayan nan sai ta tafi kasar Najeriya inda tayi digirinta na farko a fanin Shari’a a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Wanda daga bisani taje makarantar da ake horas da lauyoyi a Najeriya nanma ta kamala, sai ta koma kasar Ghana, shima haka tasamu halartar makarantar horas da lauyoyi, wanda yanzu haka tana aiki da ma’aikatar Shari’a ta kasar Ghana. Kana kuma ita matar aurece tana da ‘yaya biyu mata.

Ta kara bayyana muna cewar, tazo kasar Amrka da wani hasashe na daban, wanda daga baya sai ta gane cewar itama kasar Amrka tana da nata matsaloli, da dama sai dai kawai za’a iyacewa kawai su sunada tsari wanda suke bin doka da oda a kowane lokaci. Don haka za’aga cewar Amrka ba wai tafi kasashen Afrika bane, illa dai mu a kasashen Afrika babu kishi ne a zuciyar mutanen kasashen, wanda shike sa kasashen cikin halin da suke ciki. Ta kara dacewar a zahirin gaskiya idan da za’a dinga samun shuwagabanni irin na kasar Amrka a Afrika, to ba shakka za’a samu tsari mai nagarta a kasashen Afrka fiyema da suaran kasashen duniya.

Wani babban abun mamaki shine, daga isowarsu wanna kasa mutun na farko da yafar taronsu, ya hadamusu liyafar girma shine, Gwamnan jihar Vajiniya sun kuma samu zantawa dashi wanda yake mutun mai saukin kai matuka, kana yanuna musu cewar shugaba shine uban al’uma wanda yakamata ace kowa yayi koyi da su.

A wani bangare kuma sun samu zantawa da mutun na farko da aka fara zaba a matsayin Gwamna da yake bakin mutun a kasar Amrka, shima yabasu wasu shawarwari da yake cewa lallai duk mutun wanda ya kasance yana da juriya da naci a rayuwa to lallai zai iyacinma burinsa a rayuwa.