Wani rahoto da mujallar Journal Child Dev wacce ke bincike akan ci gaban yara, ta yi nuni da cewa yara matasa masu kimanin shekaru goma sha uku 13 ‘yan makaranta sakandire wadanda suke da rayuwar karya, musamman ma ga abokan karatunsu ‘yan mata ko maza, sukan fuskanci matsaloli da dama bayan sun kammala karatunsu na sakandire.
Dalili kuwa shine, mafi akasarin wadanna matasan sun daukarma kansu rayuwa rashin gazawa, domin kuwa basu son ace sun gaza faranta ma ‘yan uwansu rai ko da kuwa wannan halin kan kai su ga wasu matsalolin rayuwa na yau da kullum.
A lokuta da dama, matasannan kan kai ga wasu halayya na dauke-dauke da shaye-shaye da rashin da’a ga magabata, da duk wasu abubuwa da za su yi don ganin sun burge abokansu.
A cewar marubucin mujallar, Mr. Joseph Allen, irin wadanna yaran da ke yawaita son girma mace ko na namiji kan yi abota da yara wadanda suka fi su yawan shekaru, wanda ta haka sukan bude musu idonsu da wasu abubuwan da suka wuce shekarunsu. Ta haka za kaga sun san rayuwar samartaka, tun basu kai wani mataki ba.