Shugaban Hukumar Kwallon Kafar Najeriya Ya Maida Martani

Shugaban 'yan kwallon kafar najeriya

Shugaban hukumar kwallon kafar Najeriya Amaju Pinnick, ya mayar da martani kan mutanen da ke sukar sa kan tafiyar da yayi zuwa London, maimakon tsayawa gida domin kallon wasan da kungiyoyin Najeriya biyu da zasuyi wasa, amma ya ziyarci wasan Arsenal da Chelsea.

Kungiyar matasa ‘yan wasan Najeriya masu kasa da shekaru ashirin da uku, wato Super Falcons U-23 sunyi wasa ranar Lahadi wanda ya basu damar samun guri a wasannin Olympic na shekara mai zuwa in Allah ya kai mu. Wasu ‘yan Najeriya da sukayi magana a kafofin yada labarai, sunce kamata yayi ace shugaban ya ziyarci wasan Enyimba da akayi a Aba, ba wasan da akayi a London ba wanda ya kalle shi da sabon koch Sunday Oliseh.

Shi dai Pinnick an anshi ne a shafin sadarwa na Twitter alokacin wasan a filin wasa na Webley, ya dai mayar da martani a jiya Litinin inda ya bayyana cewa ya zame masa dole yace wani abu kan sukar da ake masa, ya na kuma gayawa masu sukar cewa ya ziyarci London ne domin wasu harkokin kasuwanci.

Alokacin da Pinnick yake London kungiyar Falcons tasha kashi da ci biyu da ‘daya a hannun Equatorial Guinea, ya kuma rasa damar halartar wasan matasan ‘yan kasa da shekaru 23 na neman shiga gasar Olympic ta 2016, inda aka tashi kunnen doki wanda hakan ya basu damar samun guri a gasar.