Malama Fatima Hassan, wata matashiya ce wadda tasamu damar kammala karatunta na NCE, kuma tun bayan kamala karatunta tana kokari wajen ganin tasamama kanta, sana’ar hannu don tayi kokarin dogaro da kanta. Tun bayan kamala karatunta, tana saka asusun ajiyar kayan kawa na mata wanda takanyi amfani da wasu duwatsu da suke kamar zobba.
Ta koyi wanna sana’ar ce wajen wasu makotansu, domin kuwa tana ganin cewar, kamata yayi duk lokacin da akace mutun yadawo daga aiki ko yana da wani lokaci da baya komai, to kamata yayi ya koyi wata sana’a, domin kuwa tahaka mutun zai iya tallafawa kanshi batare da jiran waniba.
Tana kara kira ga ‘yan’uwanta mata da su tashi tsaye wajen ganin sun taimakama kansu a kowane hali. Hada sana’ar hannu da aiki shine mafita ga kowace mace, mai kokarin zama wani abu a rayuwa.