Gwamnatin Jihar Naija ta Umurci Kulle Makarantu 120 a Jihar

Makarantu a jihar Naija

Sanin kowane cewar, samar da ingantacecen Ilimi ga yara, shine ginshikin rayuwa. Domin gina al’uma, ya dogare ne da yadda aka tarbiyantar da yara. Gwamnatin jihar Naija ta dauki wani salo na tsaftace makarantu a jihar.

Gwamnati jihar ta kulle sama da makarantu dari da ashirin a jihar, ta dauki wannan matakin ne a dalilin ganin cewar mafi akasarin makarantun, da ake budewa basu cika ka’idojin da suka kamata wajen samun lasisi ba. Wasu mutane kan bude makarantu batare da tuntubar hukumomiba, wanna yasa ilimi yake fuskantar barazana a jihar, ko ace a kasar baki daya.

Wasu na ganin cewar wannan matakin da gwamnarti ta dauka yayi dai dai don, kuwa ta haka ne kawai masu irin wadannan halaye na bude makarantu, da basu cika ka’idojiba zasu daina wanna hali. Ta haka kuma za’a samu nagartatun makarantu da kuma samun ingantatun dalibai a jihar dama kasar baki daya.