Ilimin Yara Nakasassu Nada Matukar Muhimanci

Yara nakasassu

Ilimin dai-daito a tsakanin yara masu bukata ta gaggawa a nan Amrka, nasamu kulawa ta musamman fiye da yadda ake tsammani. Domin kuwa a tsarin karatu irin na Amrka, a kan samama irin wadannan yaran gurabe wanda zasu gudanar da karatunsu kamar yadda sauranyara sukeyi.

Wani abun sha’awa a nan shine, ba’a banbanta wajen karatun yarannan da na masu lafiya, dom kuwa wannan kadai kan iya nunama wadannan yaran cewar, suna da banbanci da sauran yara, wanda hakan na iyasama yaran wani tunani nadaban. Za’aga cewar duk ajin yara da kashiga idan akwai yara masu bukatar taimako, zakaga cewar ana basu kulawa ta musamman.

Kuma gwamnati na taimakawa matuka wajen samamusu abubuwan more rayuwa, kamar yadda ake samama sauran yara. A wanna dalilin yasa za’agacewar a Amrka kamar basu da nakasasu ko masu bara, ba wani abune yasa hakanba illa tsari da kyautatawa ga bil’adam, ashe kuwa yakamata kowace kasa ko al’uma suyi koyi da irin wanna hali na tausayin mabukata.