Daurawa Yara Tallah na Samusu Tabin Hankali

Yan talla

Ana cigaba da kara jawo hankali iyaye, dangane da illolin sa yaransu tala. Domin kuwa masan na ganin cewar, wanna tallar na haifar da cutar tabuwan hankali ga yara masu yin talla. A tabakin Dr. Mustapha Gudaji likitan masu tabuwar hankali a Asibitin Koyarwa na Murtala da ke Kano. Masanan sun gano cewar yara da kanyi talla kan kamu da wasu cututuka da kan haifar musu da rashin natsuwa, kwanciyar hankali, yawan tunani, yawan fada da dai makamanta wadannan abubuwan.

Wanda daga bisani sukan sa su cikin wasu halaye da yakan taba lafiaya kwakwalwarsu. Mafi alkhairi shine, iyaye masu irin wanna dabi’ar su guji aiwatar da irin wanna hain, domin kuwa idan ba hakaba wanna kan iya sa iyayen cikin aikin danasani da bai da madafa.

A fahimtar wadannan likitotcin, ita wanna cutar tabin hankalin tana farawa kadan kadan ne har takaiga babba, don haka yakamata a guji sa yara cikin damuwa da wasu tunani tun da kuruciyarsu. Musamman sasu talla don basu samu damar zuwa makaranta.