Rena Sana'a Kan Haifar da Koma Bayan Matasa

Sana'ar Saida Yogot

Abun da yafi kamata da matasa shine, su kasance masu tunanin yau da gobe dama yadda zasu zamo wani abu a rayuwa. Wadannan tunanin kuwa suna samo asali ne tun a lokacin da matashi ko matashiya, suka fara tunanin yadda zasuyi wajen kokarin samama kansu abunyi.

Wani matashi mai kimanin shekaru gomasha bakwai, mai suna Shamsudeen shi dai yana sana’ar saida kayan sanyi ne, inda yake daukar kaya daga wajen wani dila, kuma yakan zagaya waje waje don tallata wanna kayan, yana saida ruwan sanyi, yogot da dai makamantan hakan.

Yana da keke nashi na kanshi, da ya siya wanda idan ya sayar da kayan da yamma sai ya kaima mai kayan kudinshi, shikuwa ya cire nashi ladan, ta haka yana samu alfanu. Wanda ta haka yake fatar yasamu ya tara kudi da zai koma makaranta nan gaba idan Allah yasa. Domin kuwa yana da sha’awar zuwa makarantar boko a nan gaba idan yasamu ya tara kudi.