Gaskiya da Adalci Garkuwan Matasa

Gyaran kwamfuta

Muhammadu Sani wani matashi ne wanda ya koyama kansa, sana’ar gyaran kwamfuta da wasu abubuwan zamani. Babban abun sha’awa da yadda yake gudanar da tashi sana’ar itace, yadda yake kokarin ganin cewar, bai sa kanshi cikin matsaloli irin yadda mafi akasarin mutane kansa kansu ciki.

Ya kan karbi gyara kuma yakanyi kokarin ganin yayi wanna gyaran a lokacin da ya kamata, kuma shi ya koya ma kanshi wannan gyaran batare da yaje makaranta an koyar dashi ba. Kuma yana ganin cewar idan dai ana maganar gyaran kwamfuta, to koda kuwa wanda yaje makaranta ba zai koyamishi wani abuba. Hasalima shi zai koyar da su domin kuwa Allah, ya bashi hazakar da basirar iya gyara a kowane mataki.

Yakan kokarta wajen kyautata dangantakarsa da jama’a, don kuwa duk aikin da akabashi yakan gaggauta gamashi cikin lokaci, idan kuwa ya samu akasi, aikin ya lalace to yakan biya batare da bata lokaciba, don kuwa bayada bukatar zuwa gaba don shari’a. Ashe kuwa wanna shine abu da yakamata ace kowane mahaluki yayi kokarin aiwatarwa a rayuwarshi ta yau da kullun.