Cigaban Kasa na Hannumu 'Yan Najeriya

Almajiri Mai Taimakon 'Yan Gudun Hijira

Jama’a musanda cewar kowane mahaluki nada irin rawar da zai taka, wajen taimakama al’umarsa a kowane irin hali. La’akari da abunda wani Almajiri mai suna Ikram Mukhtar, yayi wannan wani abune mai ban sha’awa da al’ajabi.

Wannan matashin ya sakanshi cikin harkar taimakama al’umah batare da an biyashiba, domin kuwa ya fahimci cewar yanada irin rawar da zai taka wajen, ganin ya bada tashi gudunmawa ga cigaban kasa. Su kanje sansanin ‘yan gudun hijara domin bada tasu gudunmawa, ga mabukatan da ke a wadannan wuraren, a karkashin wata kungiya da sukan samo kudaden gudunmawarsu daga wasu kasashen duniya.

Kana da ma cikin Najeriya, sukanyi amfani da shafin zumunta na facebook wajen yada manufofinsu, da kara jawo hankalin mutane da su bada tasu gudunmawa ga sauran al’umah. A irin wanna lokaci kamata yayi ace kowane matashi yayi kokari wajen bada tashi gudunmawa ga cigaban kasa ta kowane irin hali.