Hawan Sallan Sarkin Dokin Kara

Hawan sallah

Hawan sallah wata al’adar kasar Hausa ce, tun shekaru da dama da suka wuce a ke gudanar da wanna al’adar. Wanda sarki da hakimanasa kan zagaye gari domin taya al’umarsa murnar sallah. A karo na biyu wanna shekarar wasu matasa sun kirkiri wanna hawan sallahn, amma na dokin kara a tsakaninsu matasa.

Wadannan matasan sunyi kwalliya da dawakansu na kara, wannda sukayi zagaye cikin anguwannin a cikin garin Kano, sarki da sauran tawagarsa sunyi wanna hawan inda gwamna da shugaban kasa suka halarci wanna taron amma duk na yara.

A tabakin Sarkin Dokin Kara, ya bayyanar da cewar sun kirkiri wannan hawane domin koyi da magabatansu, domin kuwa wanna wani abune da yakamata ace sunyi koyi dashi kasancewar abune mai kyau. Suna kuma fatar zasu cigaba da wanna a kowace shekara. A tabakin wasu ‘yan kalo gaskiya wanna hawan ya kayatar dasu, kuma suna jin dadin yadda a ka gudanar da wanna hawan don kuwa ya nishadantar dasu matuka.