A cuci maza, wani sabon salo ne da ‘yan mata kanyi amfani da shi, wajen yaudara samari. A wannan zamanin ‘yan mata kanyi wanka da cin kwalliya sai su sa wani abu a gashinsu wanda zai nuna yadda mace ke da yawan gashi. Mafi akasarin mata sukanyi wanna daurin dan-kwalinne domin idan sukayi haka, maza suna ganin kamar yawan gashinne, amma yanzu maza sun fara gane cewar ba gashing aske bane.
Wasu ‘ynamata sun nuna nasu dalilin da yasa suke sa wanna a cuci mazan da cewar, sukan sa wanna abun ne domin su dauki hankali samari, amma wasu kuwa sunayi ne domin su gyara daurin dankwalinsu. Duk dai ta yadda mutun ya dubbi abun zaiga cewar wanna abun yakan karama ‘yanmata kyau a yayinda sukayi wanna daurin.
Wasu kuwa suna ganin wanna bai da wani asali don haka bai kamata ace mata suna wannan dabi’arba. Ai kamata yayi su bayyanar da gaskiya, domin kuwa idan ba hakaba bayan yin auren wasu abubuwa kan iya biyo baya.