Shugaban kungiyar kwallon kafar Manchester United Mr. Louis Van Gaal, ya aminta da sake sabunta kwantirakin dan wasannan Sergio Romero, a dalilin hasashen dan wasanna David De Gea kan iya barin kungiyar zuwa kungiyar Real Madrid a wanna kakar.
Kungiyar Manchester United ta tabbatar da isar mai tsaron gidannan dan kasar Ajentina da safiyar yau litinin, inda ya sa hannu a kwantirakin shekaru uku da klob in.
Dan wasan Romero dai wanda yashiga kasuwa batare da wani tarnaki ba, yace wanna chanjin shekar wani mafarkine yazamo gaskiya. Ya kuma yima Mr. Van Gaal godiya dangane da kawoshi cikin kwararru. Dan kasar Holand in dai ya bayyanar da dalilinshi na sa hannu da cewar.
A yanayinsu ganin cewar dan wasa David de Gea zai tafi kungiyar Real Madrid, sun kuma shiryama wannan kakar wasan, kana yanada tabbacin dan wasa Sergio Romero zai iya maye gurbi.