Arsenal Zata Iya Sayen Kowane Dan Wasa A Duniyar Nan In Ban Da...

Darektan kungiyar kwallon kafa ta Arsenal a kasar Ingila, Lord Harris, yace manajansu, Arsene Wenger, yana iya sayen duk dan wasan da yake so a fadin duniyar nan, domin su na da zunzuruntun kudi har dala miliyan 310 a asusunsu na sayowa ko hayar dan wasa.

Shugaban na kungiyar Arsenal wadda aka fi saninta da lakabin Gunners, yace sun fuskanci kalubale cikin ‘yan shekarun nan a gwagwarmayar neman lashe wasannin lig-lig na firimiya na Ingila, amma yana da kwarin guiwar cewa ‘yan wasansu zasu iya lashe wannan kofi.

Kungiyoyin Chelsea da Manchester United da Manchester City sun yi barin kudi sosai wajen sayen ‘yan wasa, amma kuma Karin kudin da Arsenal take adanawa ya sa ta sayi Mesut Ozil kan Fam miliyan 42 a 2013, yayin da ta sayi Alexis Sanchez kan kudi fam miliyan 35 a shekarar da ta shige. Harris yace watakila a bana ma zasu ci gaba da irin wannan zaben da vsayen ’yan wasa.

Yace sun fuskanci karancin kudi a lokacin da suka koma filin wasa na Emirates, amma a yanzu kam, asusunsu yayi nauyi, zasu iya shiga kasuwa su sayi duk dan wasan da suke so in ban da irinsu Lionel messi da Cristiano Ronaldo da aka ce kudinsu yayi tsada sosai a kasuwa.

Daya daga cikinb ‘yan wasan da aka ce Arsenal t6ana hari domin saye shine Karim Benzema, amma manajan dan wasan yace Benzema ba zai bar kungiyarsa ta yanzu ta Real Madrid ba.