Kyautatawa masoyi ko masoyiya na kara dangon soyayya, idan har anyi hakan don Allah ne. Wasu ‘yan mata dake bayyanar da nasu ra’ayin dangane da yima samarinsu hidindimu a lokuttan bukin sallah ko wasu shagulgula.
Wasu na ganin cewar ai kyautatama saurayi wajibine domin kuwa shi ke nuna kauna da fahimta a tsakani, don haka kuwa zasu iya yin hidundumu ga samarinsu ba ma kawai na abinci ba harma na dinka sutura ko wasu abubuwa makamantan hakan. Wanan wata hanyace ta fidda saurayi kunya a cikin abokansa, dacewar budurwarshi ta iya abbinci da iya kyautatawa.
Don a lokutta da dama samarin kan basu ninkin ba ninkin abun da sukayi musu hidima dashi, don jin dadin faranta masa raid a sukayi, ko na abokansa. Domin kuwa duk yadda yakasance idan baki faranta mishi rai to ba llalaibane soyayarku ta daure, domin kuwa masu iya magana kance rai dangin goro, don haka wasu na ganin zasu iya takura kansu don faranta ma samarinsu rai a kowane hali.
Allah daya ra’ayi daban, wasu ‘yan matan kuwa na ganin cewar ai wahalarda kaine mace ta tsaya tana hidima da saurayi, don kuwa kina iya gama hidima dashi ya tsallake ya koma kan wata don haka bai daceba ace mace na wahala da namijiba, kamata yayi ace namiji shike hidima ga mace. A wasu lokkutan maza ba ‘yan goyo bane, don haka suna ganin kawai shi yadace ace yayi wadannan wahalhalun har sai randa akace ya aureta kamin tayi wata hidima gareshi.