A cikin ziyara da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari, yakeyi a nan kasar Amrka, wasu dagacikin ‘yan Najeriya sunnuna irin abubuwanda suke sa ran shugaban ya maidan hankali, da kuma irin abubuwan da suke sa ran kasar Amrka zatayi wajen tallafawa kasar ta Najeriya.
Malam Abdulkadir Afaf daga jihar Gombe, yace suna kara godema kasar Amrka da irin goyon bayan da takebama sabuwar gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, wajen ganin an sama ma al’uma Najeriya yanayi mai nagarta da walwala, da fatar Allah yasa wanna kawance ya daure yakuma zama alkhairi ga talakan kasar baki daya.
Hajiya Sa’adatu Sa’ad Mustapha kaltingo, tayi kira da gwamnatin Amrka ta taimakama kasar Najeriya, wajen kwato dukiyoyin talakawa da masu rike da madafan iko sukayi waje ta ita a gwamnatocin da suka gabata, wanda tahaka ne yasa kasar take cikin talauci, da wahalahalu da mutane keciki. A kuma bangaren taimakawa wajen yaki da ‘yan ta’addar boko haram suna kara rokon gwamnatin Amrka, da ta badama shugaba Buhari duk taimakon da yakamata, wajen magance wannan matsalar, domin kuwa shi Muhammadu Buhari, kokarinshi shine ya taimakama talaka don haka yana bukatar taimakon manyya manyan kasashen duniya.
Alhaji Umaru Ali Goro ciyaman na nakasasun jihar Gombe, ya bayyanar da irin nasu rokon ga shugaban kasar Amrka da yabada kaimi wajen taimakama shugaba Buhari, wajen samama ‘yan kasar ingantacciyar rayuwa, domin daurewar domokaradiyya baki daya.