Ya Gantsara Ma Dan Fashi Cizo Ya Gutsure Masa Kunne

Wani mutumin da ake zargin dan fashi da makami ne mai suna Chijioke Ikechi na wata unguwa mai suna Ukwudara a garin Aba a Jihar Abia, ya gamu da gamonsa, inda wani mutumin da suka je zasu yi wa fashi, yayi kukan kura ya kamo dan fashin ya danne shi a kasa, sannan ya gantsara masa mummunan cizo a kunne har ya gutsure masa kunnen.

Kakakin ‘yan sandan Jihar Abia, Mr. Onyeke, yace shi Ikechi da wasu ‘yan’uwansa ‘yan fashi uku sun kai farmaki kan wani gida dake titin Ukaegbu, inda wannan lamarin ya faru.

‘Yan sanda sun kai dauki, inda sauran ‘yan fashin uku suka tsere, amma sarkin cizo ya ki sake dan fashin da ya danne a kasa ya gutsure masa kunnen hagu.

Hari la yau, Onyeke yace kafin isar ‘yan sanda, ‘yan fashi sun riga sun kwace tsabar kudi naira dubu 300 daga hannun mutanen wannan gida.

‘Yan fashin sun yi amfani da wani bututun karfe wanda aka Makala masa wani hannu na katako, kamar bindiga, suka yi amfani da shi da adduna wajen tsorata mutanen gidan.

Yanzu dai Ikechi yana hannun ‘yan sanda, yayin da yake jinyar inda kunnen nasa yake a da. Ana kuma neman sauran ‘yan fashin su uku.