Yautake jajibirin sallah a daukacin duniya, biyo bayan kamala Azumin watan Ramadana. Bisaga al’ada mutane kan kawata wanna buki a duk fadin duniya, filin Dandali ba’abarshi a baya ba wajen ganin yadda al’umah ke shirye shiryen wanna bukin sallar.
Wasu mata da muka zanta dasu sun yi muna karin haske dangane da irin farinciki da suke tattare dashi a wannan ranar, kana kuma suna kokarin su gyara kansu don nuna farinciki a wannan ranar, mafi akasarin wadannan matan na yin kitso, lalle, sababbin dunkuna da dai makamantan haka, don kuwa suna so a ranar idi su nuna banbancinta da sauran ranaku.
Makasudin wannan kwaliyar ga wasu ‘yan mata shine suyi gyaran jiki domin jawo hankalin samari a lokacin bukin, domin akasarin ‘yan mata da samari kan hadu da abokan rayuwarsu, a irin wannan lokacin. Haka kuma a bangaren matan aure sukanyi gyaran ne domin kokarin burge mazajensu, don kada su kalli wasu ‘yanmata a waje. Su kuwa matasa kanje ziyartar ‘yan uwa da abokan arziki a gidaje daban daban domin karbar barka da sallah.
A tabakin wata mai wannan sana’ar ta gyaran ‘yanmata tace bana dai abun ba harka, tana ganin kamar dai bana mutane basu da kudi, domin kuwa kasuwar tata sai godiya. Babban kira anan shine matasa maza da mata, ayi kokari ayi bukin sallah lafiaya batare da hatsaniya ba.