A kasar Hausa bukin sallah baya kammaluwa batare da hawan dawaki ba. Wani matashi Abdurahman Balarabe, wanda yayi karin haske, dangane da mahimancin dokin a lokacin bukukuwan sallah. Shi doki wani dabba ne na alfarma, da mutane kanyi amfani dashi a lokacin wasu murna a rayuwarsu. Ga matasa doki na nuna ainihin al’adu na kasar Hausa, don haka duk lokacin sallah sukan kawata dawakai suyi yawo a dokuna don nuna farincikinsu a wannan lokaci na sallah.
Ya kara dacewar, doki wani abune mai shiga rai da duk wannada yasaba dashi ba zaiso bari ba, don kuwa tun yana dan karaminshi yafara son doki, har a zuwa yanzu bayajin zai iya barin hawa doki. Wanda yana ganin ta irin haka yara kansamu kansu cikin wasu mawuyatan hali, don kuwa idan akace yaro bashi da doki kuma yanason dokin, to zai iya yin koda sata ne don yasamu yakai ga doki ko ba nashiba, wanda ta haka yakan bata tarbiyar yara.
Don kuwa ba kowane iyaye ne kan iya saya ma ‘yayansu doki ba, don kiwon doki wani abune mai matukar wahala, ciyar dashi da sauran lalurorinshi nada matukar wahala. Yayi kira da matasa suyi la’akari da cewar ba kodayaushene suke iyasamun yadda sukeso a rayuwaba, don haka kada su sama kansu tunanin abun da yafi karfinsu. Kuma suyi kokarin yin bukukuwan sallah cikin kwanciyar hankali da lumana.