A cikin ibadu da ake bukatar Musulmi ya gabatar a cikin watan Ramadana, bayaga nafilfili, sadaka, kyautatawa, da dai sauransu, akwai bukatar duk mutun mai hali ya fitar da zakkar fiddakai da ake kira “Zakkatul fitir” Wato ita wannan zakkar a na bukatar mutun ya fitar da itane kamin zuwa masallacin Idi.
Mahimmancin wanna zakkar itace, ana bada tane domin a taimakama mabukata masu karamin karfi, a karshen wannan watan azumin, domin su samu abun da zasu ciyadda iyalansu, da rage yawan barace barace ga marasa hali. Ita dai wannan zakar tana koyama masu hali tausayi wajen taimakama marasa karfi. Kana kuma bada wanna zakkar wata hanyace ta nuna godiya ga Allah, da rahamarsa a wannan wata mai falala.
A Karin haske da Dr. Adam Abubakar, na kwalegin tsangayar Shari’a ta Kano, yayi Karin haske dangane dasuwa Al-Qur’ani ya bayyanar da cewar akwai kashin mutane takwas su suka kamata a ba zakkar, musakai, talakawa, ma’abota wasu addinai don kwadaitar dasu zuwa ga Musulunci, da makamantansu. Da fatar al’umah zasu maida hankali wajen kyautata ibadunsu.