Matasa na Bincike Mai-Zurfi a Shafin Face Book

Shafin Face book

Bincike ya nunar da cewar, matasa na amfani da shafin sada zumunci na Facebook, wajen ilmantar da kansu da nagartattun, muhimman darussa, batare da sunje makaranta ba. Matasannan kan sakansu cikin wasu mahawarori da wasu kan rubuta a shafinsu na Facebook in, wanda za’aga cewar matasa kan bada tasu fahimtar, wanda take dai-dai ko take fin ta wadansu yara ma da sukaje makaranta.

Mafi akasarin tattaunawar da matasannan kanyi ta sa kai, na maida hankaline a fannin bincike na kimiyya da fasaha. A cewar wannan marubucin Mr. Cheistine Greenhow, Ita tattaunawar sakai da matasa kanyi, na kara fahimta garesu a wasu darussa masu wuyar koyo. Domin kuwa shafin Facebook ba kawai don zumunci aka kirkireshiba, harma da ilmantar da juna wasu abubu na dan-daban daga wata nahiyar zuwa wata.