WASHINGTON, DC —
Rundunar sojojin Najeriya ta damke wani mutumin da ta ce shine kanwa uwar gami wajen kitsa hare-haren ta'addancin da aka kai kan wani masallaci da gidan abinci a garin Jos, da kuma wata ma'aikata a garin Zariya dake Jihar Kaduna.
Kakakin runduna ta 7 ta sojojin Najeriya, Kanar S.K. Usman, yace an damke wannan mutumin tare da wasu 'yan ta'addar su biyu sun batar da kama cikin wata babbar mota, a inda ake binciken ababen hawa a garin dadinkowa dake Jihar Gombe.
Yace mutanen su na can su na amsa tambayoyi.
Kanar Usman ya roki jama'a da su rika sanya idanu sosai, su kuma sanar da hukumomin tsaro idan sun ga duk wani mutumi ko al'amarin da ba su yarda da shi ba.